ABNA24 : Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran Sa’id Khatib Zadeh wanda ya gabatar da taron manema labaru a yau Litinin ya mayar da martani akan wasu rahotanni da suke nuni da cewa; An bude tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka a kasar Oman, sannan ya kara da cewa:
“ Trump ba ya fahimtar dabi’ar alakar kasa da kasa, haka nan kuma masu bashi shawara.”
Har ila yau kakanin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kara da cewa:
“ Wajibi ne ga Trump ya yi furuci da kurakuren da ya yi, ya kawo karshen wannan yakin da yake yi akan ‘yan’adamtaka, ya kuma biya dukkanin al’ummar Iran dukkanin asarar da ya haddasa musu ta hanyar yakin da shela akansu.”
342/